'Yan Sandan Taraba Sun Tabbatar Da Kama Kwamandojin Boko Haram 2
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2860-'yan_sandan_taraba_sun_tabbatar_da_kama_kwamandojin_boko_haram_2
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba a Nijeriya ta tabbatar da kama wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram guda 2 wadanda aka jima ana nemansu inda ta ce tuni ta mika su ga sojoji a jihar.
(last modified 2018-08-22T06:58:01+00:00 )
Mar 24, 2016 04:49 UTC
  • 'Yan Sandan Taraba Sun Tabbatar Da Kama Kwamandojin Boko Haram 2

Rundunar 'yan sandan jihar Taraba a Nijeriya ta tabbatar da kama wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram guda 2 wadanda aka jima ana nemansu inda ta ce tuni ta mika su ga sojoji a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Taraban Shaba Alkali ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce sun sami nasarar kama kwamandojin su biyu Ali Audu wanda aka kama shi a Tella, na karamar hukumar Gassol, sai kuma Abdulmumini Abdullahi wanda aka kama a karamar hukumar Balli.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa tuni suka mika mutane biyun wadanda ya ce an kama su ne a lokuta mabambanta ga rundunar sojin Nijeriya da ke jihar Yobe don ci gaba da tsare su da kuma gudanar da bincike kansu.

A wata sabuwa kuma sojojin Nijeriyan sun sanar da samun nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar Boko Haram din guda biyar da kuma kubutar da wasu mata da maza da kananan yara kimanin 180 da suka yi garkuwa da su a wasu hare-hare da sojojin suka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno.