Ci Gaba Da Karuwar Tashe-Tashen Hankula A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo
(last modified Tue, 27 Feb 2018 05:21:53 GMT )
Feb 27, 2018 05:21 UTC
  • Ci Gaba Da Karuwar Tashe-Tashen Hankula A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta baya -bayan nan ta rikide zuwa tarzoma a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar lamarin da janyo hasarar rayukan mutane da jikkatan wasu adadi na daban.

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta hana gudanar da duk wani taron gangami ko zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Joseph Kabila, inda a zanga-zangar baya- bayan nan aka samu hasarar rayukan mutane masu yawa. Rahotonni sun bayyana cewa: A zanga-zangar ranar 31 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ta 2017 da kuma ta ranar 21 ga watan Janairun wannan shekara ta 2018 mutane akalla 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon farmusu da jami'an tsaron kasar suka yi.

Har ila yau a matakin da 'yan darikar katolika ta mabiya addinin Kirista suka dauka na jaddada rashin amincewarsu da babakeren shugaba Joseph Kabila a kan karagar mulkin kasar ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Kinshasa a ranar Lahadin da ta gabata, zanga-zangar ta fuskanci maida da martani mai gauni daga jami'an tsaron kasar, inda suka kashe mutane akalla biyu tare da jikkata wasu adadi na daban.

A fili yake cewa: Matakin da shugaba Joseph Kabila ya dauka na rashin gudanar da zaben shugabancin kasa tun bayan da wa'adin shugabancinsa na biyu kuma na karshe ya kare a ranar 20 ga watan Disamban shekara ta 2016; dambaruwar siyasa ta fara kunno kai a kasar, amma hukumar zaben kasar ta gabatar da wasu uzurori tare da sanar da jinkirta zaben zuwa farkon wannan shekara ta 2018, inda a halin yanzu haka mahukuntan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ke neman sake dage lokacin zaben shugabancin kasar zuwa wani lokaci nan gaba.

Manazarta kan harkokin siyasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da masu fashin bakin siyasar yankin suna ganin Joseph Kabila da jam'iyyarsa ce ke son ganin sun ci gaba da gudanar da jagorancin kasar, kuma wannan mataki nasu yana samun goyon baya daga abokan huddarsu na kasashen yammacin Turai musamman kasashen Faransa da Belgium. Kamar yadda daga cikin makirce-makircen da suke kitsawa da nufin ganin Joseph Kabila ya ci gaba da jan ragamar shugabancin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo domin kare musu masalaharsu, akwai furucin da babban kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Derrick Mgwebi ya yi cewa: Matukar ba gwamnatin Joseph Kabila ba ce ke jan ragamar shugabancin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, to babu shakka kasar zata ci gaba da fuskantar matsalolin tashe-tashen hankula.

A halin yanzu dai gwamnatin Joseph Kabila tana ci gaba da da'awar cewa: Zata gudanar da zabuka a kasar a cikin wannan shekara ta 2018, inda a gefe guda kuma take ci gaba da murkushe masu fafatukar ganin an gudanar da zabukan. Kamar yadda masu fashin bakin siyasa suke ganin har yanzu babu wani gagarumin shirin da gwamnatin Joseph Kabila take yi na gudanar da tsabtaceccen zabe a kasar.