An Fara Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Mulki A Burkina Faso
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28619-an_fara_shari'ar_wadanda_ake_zargi_da_juyin_mulki_a_burkina_faso
Yau Talata, an fara shari'ar wandanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a watan Satumba na 2015 a Burkina Faso.
(last modified 2018-08-22T11:31:29+00:00 )
Feb 27, 2018 11:17 UTC
  • An Fara Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Mulki A Burkina Faso

Yau Talata, an fara shari'ar wandanda ake zargi da yunkurin juyin mulki a watan Satumba na 2015 a Burkina Faso.

Mutanen da ake zargin sun hada da wasu manyan janar biyu, wato Gilbert Diendere da kuma Djibril Bassole, wadanda na hannun daman tsohon shugaban kasar Blaise Compaore ne.

Baya gare su da akwai kuma mutane kimanin 80 da ake zargi da cin amanar kasa, kisa, raunanawa da kuma lalata dukiyar kasa. 

Wasu majiyoyin shari'a sun ce wadanda ake zargin na fuskantar hukunci mai tsanani a yayin shari'a da za'a kwashe watanni ana yi.