Nijar : An Kame Lita 300,000 Na Man Fetur Din Sumogal
Jami'an kwastom a birnin Yamai na Jamhuriya Nijar, sun kame sama da Lita 300,000 na man fetur din sumogal da aka shigo da shi daga Najeriya.
An dai kame man fetur din daga hannun 'yan bunburutu dake sayar da shi kan tituna, tare da cafke masu sayar da shi da dama.
Wannan dai na daga cikin matakin da hukumomin kasar suka dauka na dakile safara da kuma sayar da man na 'yan bunburutu a babban birnin kasar.
Tun a shekara 2011 ne Nijar, ta soma fitar da man fetur din ta, saidai shigo da shi daga makofciyar kasar Najeriya, don sayar da shi kasa da farashin gwamnati na haifar wa da kasar hasara bilyoyin kudaden CFA na haraji.
Bayanai daga kasar sun ce ana zargin manya manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa da hannu a wannan harka ta sumogal din man fetur.