An Dage Shari'ar Wadanda Ake Zargi Da Juyin Mulki A Burkina Faso
Feb 28, 2018 11:13 UTC
A Burkina Faso an dage zaman shari'ar wadanda ake zargi da yunkurin kifar da gwamnati a watan Satumba na 2015, da aka fara a jiya Talata.
An dai dage shari'ar har zuwa tsakiyar watan Maris mai zuwa.
Matakin dage shari'ar dai ya biyo bayan da dukkan lauyoyin wadanda ake zargin suka fice daga zauren shari'ar, sa'o'i hudu da soma zaman, saboda rashin gamsuwa da adalcin kotun sojin.
Saidai a cewar lauyen masu kara, wannan wani yunkuri ne na jan shari'ar ta yadda za ta dauki dogon lokaci.
Tags