An Kai Hari Ouagadougou Babban Birnin Burkina Faso
(last modified Fri, 02 Mar 2018 18:56:45 GMT )
Mar 02, 2018 18:56 UTC
  • An Kai Hari Ouagadougou Babban Birnin Burkina Faso

Wasu ‘yan bindiga sun buda wuta a kusa da ofishin jadakancin kasar Faranda da ke Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso, kafin daga bisani su wuce zuwa shalkwatar tsaron kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto wata majiyar kasar dake nuni da cewa ‘yan bidiga 5 ne a cikin watan mota, suka buda wuta a kan jama’ar da ke wucewa a kan titi, daga nan kuma suka doshi ofishin jakadancin Faransa suna cigaba da harbe-harbe.

Wasu mutane da kusa da anguwar da lamarin ya faru sun bayyana cewa sun ji karar wata fashewa a harabar shalkwatar tsaron kasar.

Jean-Marc Châtaigner jakadan kasar Faransa a kasar Iviry Coast ya bayyana harin da aka kai  wannan juma'a a matsayin harin ta'addanci.

Wannan dai ba shi ba ne karo na farko da  birnin  Ouagadougou ke fuskantar irin wannan  hare-hare daga ‘yan bindiga , ko a shekarun da suka gabata ma birnin ya fuskanci irin wadannan hare-hareda ya yi sanadiyar hallakar  rayukan jama’a da dama.