Zimbabwe: Babbar Jam'iyyar Adawa Ta Fitar Da Dan Karar Neman Shugabancin Kasa
Bababr jam'iyyar adawa a kasar Zimbabwe MDC ta fitar da dan takararta a zabe shugaban kasa da a za a gudanar a kasar a cikin wannans hekara ta 2018.
Shafin jaridan kasar Faransa ta Lomond ya bayar da rahoton cewa, jam'iyyar MDC ta tsayar da sabon shugabanta Nelson Chamisa a matsayin dan takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.
An zabi Nelson Chamisa a matsayin sabon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Movement for Democratic Change MDC a takaice ne, bayan rasuwar tsohon shugaban jam'iyyar Morgan Tsvangirai a ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata a kasar Akasar Afirka ta kudu.
A cikin wannan shekara ta 2018 ce dai ake sa ran za a gudanar da zaben shugaban kasar ta Zimbabwe, inda mutane miliyan 3 da dubu 500 suka cancanci kada kuri'a.