Turkiyya : Erdogan Ya Kammala Ran Gadinsa A Afrika
Shugaba Racep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya kammala gajeren ran gadin da ya kaddamar a wasu kasashen nahiyar AFrika.
Tun daga Mali inda ya kawo karshen ziyara ta sa, shugaba Erdogan ya yi allawadai da harin Ouagadugu na Burkina Faso, tare da jaddada goyan bayansa ga kasar Mali akan yakin da take da ta'addanci.
A yayin da ya ziyarci kasar Mauritaniaa ranar Laraba data gabata, Erdogan, ya sanar da alkawarin kasarsa na taimaka wa kungiyar kasashen yankin G5 Sahel da dalar Amurka bilyan biyar.
A farkon wannan mako mai shirin karewa ne shugaban kasar ta Turkiyya, ya kaddamar da gajeran ran gadin a nahiyar AFrika, wanda ya kai kasashen Aljeriya, Mauritaniya, Senegal da Mali.
A yayin ziyarar Turkiyya ta kulla yarjejeniyoyi da dama da wadannan kasashen, a bangaren makamashi, ilimi, tattalin arziki da inganta huldar diflomatsiyya.