An Kashe Sojin Senegal Guda A Kudancin Kasar
(last modified Tue, 06 Mar 2018 06:28:05 GMT )
Mar 06, 2018 06:28 UTC
  • An Kashe Sojin Senegal Guda A Kudancin Kasar

Dakarun tsaron kasar Senegal sun sanar da kashe jami'insu guda a yankin Casamance na kudancin kasar

Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, Rundunar tsaron kasar ta Senegal ta ce a yayin wani farmaki da sojojin kasar suka kai yankin Casamance na kudancin kasar da nufin  tsarkake shi daga 'yan tawaye, wani soja guda ya rasa ransa yayin da wani da daban ya jikkata.

Wannan farmaki na zuwa ne, bayan wani hari da 'yan tawaye suka kai yankin a watan janairun da ya gabata tare da kashen fararen hula 14.

Sanarwar ta Rundunar tsaron kasar ta ce, manufar kai wannan farmaki, tsarkake yankin daga 'yan tawaye, da sansanin da suka kafa a yankin, da kuma kawo karshen masu sarar itace ba kan ka'ida ba a tsaunukan yankin Bayotte.

A yayin wannan farmaki sojojin kasar sun samu nasarar kame 'yan tawaye biyu tare da mika su a hanun jami'an jandarma na yankin, kuma an samu wasu makaman yaki a yayin da aka kwace sansanin 'yan tawayen a kauyen Ahega.

Har ila yau sanarwar ta ce sojoji za su gaba da zama a yankin domin kare rayukan masu kai da kawo da dukiyoyinsu a yankin.