Kenya : Uhuru Ya Gana Da Jagoran 'Yan Adawa
Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya, ya gana da jagoran 'yan adawa na kasar Raila Odinga a karon farko tun bayan sake zabensa a matsayin shugaban kasar a watan Oktoba.
Bangarorin biyu dai sun yi alkawarin lalubo hanyoyin sansanta 'yan kasar, a wani taron manema labarai a ofishin shugaban kasar dake Nairobi.
Ganawar mutanen biyu ta zo ne dai sa'o'i kadan gabanin ziyarar aiki da sakataren harkokin wajen Amurka, rex Tillerson ya kai a birnin Nairobi.
Kafin hakan dama Amurkar ta sha kiran mutanen biyu da basa ga maciji da juna dasu gana domin fitar da kasar daga cikin rikicin siyasa.
Zabukan shugaban kasa da aka gudanar a shekara 2017 da ta gabata, sun fuskanci kalubale da dama, inda na farko aka soke shi, sai na biyu kuma wanda 'yan adawa suka kaurace wa.