An Cafke Jagororin 'Yan Adawa Biyu A Senegal
Mar 09, 2018 15:00 UTC
'Yan sanda a birnin Dakar na Senegal na tsare da wasu jagororin 'yan adawa biyu, a yayin wata zanga-zanga da hukumomin kasar suka haramta.
Jagororin biyu sun hada da Umar Sarr na jam'iyyar (Senegalese Democratic Party), da kuma Mamadu Diop Decroix na gamayar wasu jam'iyyun adawa a kasar (AJPADS).
Kafin hakan dai 'yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa kwalla, don tarwatsa haramtaciyyar zanga-zangar a yau Juma'a.
Masu adawa da shugaban kasar ta Senegal, Macky Sall, na bukatar ministan cikin gida na kasar Aly Ngouille Ndiaye da yayi murabus akan aikinsa.
Tags