Ziyarar Aikin Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Rasha Ya Kai Zuwa Habasha
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya fara gudanar da ziyarar aiki a kasar Habasha, inda zai gana da mahukuntan kasar a kan batutuwa da dama musamman a fagen bunkasa harkar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.
Ziyarar aikin Sergei Lavrof zuwa kasar Habasha yana daga cikin shirin gwamnatin Rasha na ganin ta bunkasa alakarta da kasashen Afrika a bangarori da dama musamman a bangaren tattalin arziki, siyasa da tsaro .. A fuskar tattalin arziki tuni kamfanonin kasar Rasha musamman a bangaren man fetur da iskar gas da kuma makamashi suka bayyana shirinsu na baje kolinsu a kasashen nahiyar Afrika tare da kulla yarjejeniya ta tsawon lokaci da kasashen. Kamar yadda mahukuntan Rasha suke ganin lallai bunkasa harkar tattalin arziki da gudanar da taimakekkeniya a tsakaninsu da kasashen nahiyar Afrika musamman kasar Habasha ke da muhimmanci da zai kai ga habakar ci gaba ga dukkanin bangarorin biyu.
A bangaren siyasa da tsaro kuwa; kasar Rasha tana kokarin ganin ta daukaka matsayinta tare da samun karin karbuwa a tsakanin kasashen Afrika musamman ganin yadda kasar ta Rasha ta yunkuro a fagen taimakawa kasashen Afrika a harkar tsaro ta hanyar yaki da ta'addanci musamman a yankin arewacin Afrika. Kamar yadda gwamnatin Rasha ta kulla yarjejeniya a bangarori da dama da kasashen Afrika kan sayar musu da makamai da jiragen saman yaki misalin kasashen Aljeriya, Sudan, Masar da sauransu.
Sakamakon haka a fili yake cewa: Ziyarar aikin da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrof ya fara gudanarwa a nahiyar Afrika musamman a kasar Habasha a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Rex Tillerson ke gudanar da ziyarar aiki a wasu kasashen nahiyar: za a iya dubarta a mahanga biyu: Mahanga ta farko ita ce: Irin muhimmancin da kasashen nahiyar Afrika suke da shi a wajen manyan kasashen duniya da kuma kokarin da kowane bangare ke yi na ganin ya samu damar shimfida kolinsa a nahiyar.
Mahanga ta biyu ita ce: Ziyarar Sergei Lavrof zuwa kasar Habasha da nufin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu musamman a fagen tattalin arziki duk kuwa da kasancewar Habasha a matsayar kawar kasar Amurka lamarin da ke nuni da cewa mahukuntan Rasha suna ganin akwai wata gagarumar rawar da zasu taka a kasar musamman a harkar tattalin arziki da ma tsaro domin janyo hankulan mahukuntan Habasha zuwa gare su.