Gabon Ta Sanar Da Anniyar Janye Sojojinta Daga Tawagar MINUSCA
(last modified Sun, 11 Mar 2018 05:51:08 GMT )
Mar 11, 2018 05:51 UTC
  • Gabon Ta Sanar Da Anniyar Janye Sojojinta Daga Tawagar MINUSCA

Kasar Gabon ta sanar da aniyarta ta janye sojojinta 450, daga cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, dake aiki a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.

Wata sanarwa da gwamnatin Gabon ta fitar, ta ce matakin ya biyo bayan samun sukuni da zaman lafiya a wannan kasa ta Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.

Saidai wani jami'in MDD a birnin New York, da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce matakin ya biyo bayan samun bayyanai na rashin yin biyaya da sojojin Gabon din suka nuna, da kuma zargin cin zarafin mata.

Matakin janye sojojin na Gabon idan ya tabbata, babban kalubale ga tawagar ta Minisca, wacce a shekara 2017 data gabata kwamitin tsaro na MDD ya amunce kara ta da yawan tawagarta da dakaru 900.

Kafin hakan dai MDD,  ta ce tana mutunta zabin na gwamnatin ta Gabon, kuma tuni aka fara tattaunawa kan jadawalin janye dakarun Gabon din a cikin lokacin da ya sawaka.