Tattalin Arzikin Arewacin Afirka Ya Bunkasa Da Kashi 4.9
Bankin bunkasa tattalin arzikin Afirka ya sanar da cewa kashi 4.9 na arzikin kasashen arewacin Afirka ya bunkasa a shekarar 2017 din da ta gabata.
Cikin wani rahoto da ya fitar a wannan talata, Bankin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ya cea shekarar 2017 din da ya gabata tattalin arzikin kasashen arewacin Afirka ya karu da kashi 4.9 kuma idan aka kwatamta da shekarar 2016, da arzikin kasashen ya bunkasa da kashi 3.3, an samu ci gaba sosai wajen bunkasar tattalin arzikin a shekarar 2017 din da ta gabata.
Rahoton ya ce bayan kasashe yankin gabashin Afirka, kasashen arewacin Afirka ne suka fi bunkasa a fanin tattalin arziki cikin shekarar 2017.
Har ila yau rahoton ya ce kasashen yankin arewacin Afirkan sune a sahun farko wajen bunkasar yawan al'umma, yayin da kasashen yankin yammacin Afirka suka zo a matsayi na karshe.