An Yanke Hukuncin Kisa Kan Wasu 'Yan Ta'adda 12 A Aljeriya
Wata kotu a kasar Aljeriya ta yanke hukuncin kisa kan wasu 'yan ta'adda 12 a kasar
Tashar Talabijin din Aljazeera ta habarta cewa kotun hukunta manyan laifuka ta Kasantin a kasar Aljeriya ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 12 bayan da ta same su da laifin kafa wata kungiyar 'yan ta'adda mai alaka da alka'ida ta yankin arewacin Afirka da kuma aiki da shahararen dan ta'adda nan Abdul-Malik Daruklan.
Rahoton ya ce daga cikin sunayen da aka fitar wadanda aka yankewa wannan hukunci, akwai Abdul-Malik Daruklan shugaban kungiyar Alka'ida na yankin arewacin Afirka, da Mus'ab Abdul wadud da Mukhtar bn Mukhtar dukkaninsu jagorori ne na kungiyar Alka'ida a yankin arewacin Afirka.
Jaridar Alkhbar ta kasar Aljeriya ta wallafa cewa daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisan akwai mutum uku 'yan asalin kasar Murtaniya da kuma wani tsohon jami'in jandarma na kasar.