Shugaba Buhari Ya Gana Da Iyayen 'Yan Matan Dapchi Da Aka Sace
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da iyayen 'yan matan sakandaren Dapchi da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace a kwanakin baya.
A jiya Laraba ne dai shugaba Buhari ya kai ziyara a jahar Yobe, a ci gaba da ziyarar da yake a yankunan da ake fama da rikici, inda bayan ganawa da sarakunan gargajiya a birnin Damaturu, Buhari ya nufi garin Dapchi.
Iyayen yaran da aka sace dai sun hallara ne a makarantar da aka sace yaran, inda shugaba Buhari ya same su kuma ya yi musu jawabi.
Daga cikin abubuwan da ya jaddada a jawabin nasa har da bin dukkanin hanyoyin da suka dace domin kubutar da 'yan matan da aka sace, inda ya ce ko da wasa gwamnati ba zata kasa a gwiwa ba kan wanann batu.
Yayin da wasu suke jinjina wa shugaba Buhari dangane da wadannan ziyarori da yake kaiwa a halin yanzu a irin wadannan yankuna, wasu kuma suna bayyana hakan da cewa magana ce ta siyasa kawai, tare da danganta hakan karatowar lokacin zabe.