Jam'iyyar Annahadha Ta Tunusiya Bata Goyon Bayan Rusa Gwamnatin Kasar
Shugaban Majalisar Shawara ta Jam'iyyar Annahadha ta kasar Tunusiya ya fitar da sanarwar cewa; Jam'iyyarsu bata goyon bayan shirin rusa gwamnatin da fira minista Yusuf Shahid ke jagoranta a kasar.
Shugaban Majalisar Shawarar ta Annahadha Abdul-Karim Al-Haruni ya bayyana cewa: Akwai yiyuwar jinkirta gudanar da bincike kan ayyukan gwamnatin Tunusiya zuwa bayan gudanar da zabukan 'yan Majalisun kananan hukumomin kasar a watan Mayun wannan shekara; Yana mai fayyace cewa: Rusa gwamnatin kasar a halin yanzu zata iya janyo bullar matsala a zabukan kananan hukumomin kasar.
Al-Haruni ya jaddada cewa: Jam'iyyarsu ta Annahadha tana da ra'ayin cewa gwamnatin Tunusiya ta samu nasarori a harkar tabbatar da tsaro da siyasa, kuma a nan gaba irin rawar da gwamnatin ke takawa a fagen bunkasa harkar tattalin arziki zata bayyana.
A ranar uku ga watan Agustan shekara ta 2017 da ta gabata ce shugaban kasar Tunusiya Baji Qa'id Al-Sibsi ya bada umurnin kafa sabuwar gwamnati a kasar karkashin jagorancin fira minista Yusuf Shahid,inda tun bayan kafa gwamnatin ta zage dantse a fagen yaki da ta'addanci da rashin aikin yi a kasar.