Nijar : Malumman Jami'ar Yamai Sun Koma Bakin Aiki
A jamhuriya Nijar, yau Litini ne malumman jami'ar birnin Yamai ke komawa bakin aiki bayan shafe kusan wata guda suna gudanar da yajin aiki.
A ranar 20 ga watan Fabarairu ne kungiyar malumman jami'ar ta (SNECS) ta tsunduma yajin aikin din dindin sakamakon duka da cin zarafin wani malamin jami'ar da daliban jami'ar sukayi.
Tun lokacin ne kuma malumman jami'ar suka bukaci a rusa kungiyar tabbatar da tsaro da da'a ta daliban (CASO), wacce mambobinta ne suka ce suka duki malamin.
Dage yajin aikin malumman dai ya biyo bayan wata tattaunawa da ma'aikatar ilimi mai zurfi ta kasar ta yi da kungiyar malumman jami'ar a ranar Asabar data gabata inda kuma hukumomin kasar suka amunce rusa kungiyar ta CASO kamar yadda malumman suka bukata.
Mahukuntan kasar sun kuma sha alwashin samar da tsaro ga malumman jami'ar ta Yamai a bakin aiki.