Kasashen Gabashin Afirka Sun Sanar Da Matakan Fada Da Ta'addanci A Yankinsu
A kokarin da ake yi na tabbatar da tsaro da kawo karshen hare-haren ta'addanci, shugabannin hukumomin tsaro da leken asiri na kasashen Gabashin Afirka sun gudanar da wani taro a kasar Uganda.
Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radio da Talabijin na Iran ya jiyo mataimakin kwamandan dakarun kare kasa na kasar Uganda, Wilson Mbadi, a wata tattaunawa da yayi da manema labarai yana fadin cewa a yayin wannan taron da aka gudanar da shi a birnin Kamfala babban birnin kasar Uganda, shugabannin hukumomin tsaron kasashen Gabashin Afirka sun yi musayen ra'ayi kan batun tsaron kasashensu.
Mr. Mbadi ya ce manufar taron dai ita ce kokari wajen samo hanyoyin fada da ta'addanci da toshe hanyoyin da 'yan ta'adda suke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu a yankin Gabashin Afirkan, ta hanyar musayen bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaron wadannan kasashen.
Shugabannin hukumomin tsaro da leken asiri na kasashen Uganda, Kenya, Tanzaniya, Rwanda, Somaliya, Mauritius. Sudan, Sudan ta Kudu, Djibouti, Comoros da kuma Madagaskar ne suka halarci taron.