Uganda: Kasashen Gabashin Afirka Sun Yi Taro AKan Harkokin Tsaro
(last modified Tue, 20 Mar 2018 12:06:47 GMT )
Mar 20, 2018 12:06 UTC
  • Uganda: Kasashen Gabashin Afirka Sun Yi Taro AKan Harkokin Tsaro

Taron na birnin Kampafa ya hada manyan jami'an tsaro da leken asiri da suka fito daga kasashen yankin gabashin Afirka.

Mataimakin babban kwamandan jami'an tsaron kasar Uganda, Wilson Mbadi ya fadawa manema labaru cewa; Kasashen yankin gabashin Afirka suna kokarin kawo karshen ayyukan ta'addanci ne daga yankin, ta hanyar musayar bayanan asirai a tsakaninsu. Haka nan kuma gano kungiyoyin 'yan ta'addar da ake da su.

Kasashen da suke halartar taron sun kunshi Uganda, Kenya, Tanzania, Rwanda, Somaliya, Sudan Ta Kudu, Sudan. Sai kuma kasashen Djibouti da Komoro da Madagascar.

Taron dai zai dauki kwanaki biyu ne ana yin sa.