Najeriya: An Sako Wasu Daga Cikin 'Yan Matan Dapchi A Yau Laraba
Mar 21, 2018 11:57 UTC
Rahotanni daga Najeriya na cewa an sako wasu daga cikin 'yan matan Dapchi da mayakan Boko Haram suka sace.
A wata sanarwa da ma'aikatar watsa labaran Najeriya ta mika wa manema labarai dazu-zadun nan, ta tabbatar da cewa a yau an saki 'yan mata 76 daga cikin 'yan mata 110 da Boko Haram suka sace a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Kafin fitar da wannan sanarwa a 'yan sa'oin da suka gabata, kafofin yada labarai da dama a Najeriya sun yi ta bayar da rahotanni a yau da ke cewa; an saki 'yan mata 105 ne, yayin da biyar daga cikinsu kuma ake cewa sun mutu.
Tags