Martanin Majalisar Malaman Aljeriya Kan Fatawar Masu Kafurta Musulmi
(last modified Wed, 21 Mar 2018 12:01:09 GMT )
Mar 21, 2018 12:01 UTC
  • Martanin Majalisar Malaman Aljeriya Kan Fatawar Masu Kafurta Musulmi

Majalisar malaman addinin muslunci a kasar Aljeriya ta mayar da martani kan fatawar da babban malamin 'yan salafiyya na kasar ya bayar, da ke kafirta wani bangaren musulmi.

A cikin bayanin da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Aljeriya ta fitar a jiya, ta bayyana cewa nauyi ne da ya rataya  a kan gwamnatin kasar da ta dauki matakan ladabtar da masu neman haifar da rashin jituwa tsakanin al'umma.

A cikin fatawar da babban malamin wahabiyawa 'yan salafiyya na kasar Aljeriya Muhammad Ali farkus ya bayar, ya bayyana mabiya darikun sufaye da kuma 'yan siyasa da cewa kafurai ne, tare da bayyana cewa duk wani dan sunna da ya shiga siyasa ko ya mara baya ga wani dan siyasa ya fita daga musulunci.

Majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Aljeriya ta bayyana wannan fatawa da cewa tana da matukar hadari, kuma ba fatawa ce da ta ginu a kan dalilai na hankali ba, balanata hujjoji na addinin musulunci.

Akasarin al'ummar kasar Aljeriya dai mabiya darikin sufaye ne, musamnan ma mabiya darikar Tijjaniya, wadda tafi samun karbuwa  a tsakanin al'ummomin kasar.