Najeriya : 'Yan Matan Makarantar Dapchi 101 Boko Haram Ta Sako
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29278-najeriya_'yan_matan_makarantar_dapchi_101_boko_haram_ta_sako
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa 'yan matan makarantar sakadaren Dapchi 101 ne kawo yanzu kungiyar Boko Haram ta sako daga cikin 110 da kungiyar ta yi garkuwa dasu.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Mar 21, 2018 16:02 UTC
  • Najeriya : 'Yan Matan Makarantar Dapchi 101 Boko Haram Ta Sako

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa 'yan matan makarantar sakadaren Dapchi 101 ne kawo yanzu kungiyar Boko Haram ta sako daga cikin 110 da kungiyar ta yi garkuwa dasu.

Tunda farko dai an sanar da sako 'yan matan 76, amma a wata sanarwa da ministan yada labarai na kasar Lai Muhammad ya aike wa manema labarai an ce adadin 'yan matan da aka sako ya kai 101.

Wasu rahotannin na daban sun ce biyar daga cikin 'yan matan sun mutu.

Kawo yanzu dai jami'an tsaro sun fara tattara 'yan matan don duba lafiyarsu, kuma nan gaba ake sa ran shugaban kasar Muhammadu Buhari zai gana dasu a cewar wasu rahotanni.

Babu dai wani karin bayyani da gwamnatin Najeriyar ta yi kan yadda aka sako 'yan matan ko kuma ta ya aka maido su gida.

A ranar 19 ga watan Fabrairu da ya gabata ne mayakan na Boko haram suka sace 'yan matan su 110 a makarantar kwana dake garin Dapchi a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.