Mar 24, 2018 06:31 UTC
  • Babbar Jam'iyyar Adawa A Sudan Ta Bukaci Murabus Din Shugaban Kasar

Jam'iyyar Ummah da take matsayar babbar jam'iyyar adawa a Sudan ta bukaci shugaban kasar Umar Hasan Albashir kan ya dauki matakin yin murabus daga kan karagar shugabancin kasar.

Jaridar Al-Qudus Arabi ta habarta cewa: Shugaban babbar jam'iyyar adawa a Sudan ta Ummah Sadiq Al-Mahdi ya bukaci shugaban kasar Umar Hasan Albashir da ya hanyar ruwan sanyi ya yi murabus daga kan karagar shugabancin kasar domin kasar Sudan ta zauna lafiya.

Al-Mahdi ya kara da cewa: Dole ne a kan shugaba Umar Hasan Albashir ya yi murabus daga kan mukaminsa, kuma kafin nan ya bada umurnin sakin dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su a gidajen kurkuku tare da shimfida hanyar kawo karshen duk wasu tashe-tashen hankula a kasar musamman matsalar kungiyoyin 'yan tawaye.

Shugaban jam'iyyar adawar ta Ummah ya jaddada cewa: Al'ummar Sudan suna shirye su dauki matakin gudanar da bore da kasar bata taba ganin irinsa ba a tsawon tarihinta, don haka irin wannan bore zata iya kawo karshen gwamnatin kasar, sakamakon haka hanya mafi sauki ita ce yin murabus daga kan karagar shugabancin kasar ta hanyar ruwan sanyi.

Shugaban kasar ta Sudan dai yana fuskantar tuhumce-tuhumce a kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifuka a duniya da ke birnin Hek da suka hada da tafka laifin yaki da cin zarafin bil-Adama a yankin Darfur da ke yammacin kasar. 

Tags