Najeriya : An Mika 'Yan Matan Dapchi Ga Hannun Iyayensu
Hukumomi a Najeriya sun mika 'yan matan nan na makarantar sakandaren Dapchi a hannun iyayensu a yau Lahadi.
Bayanai daga yankin sun ce iyayen daliban da abokan arziki da jama'ar garin sun tarbi 'yan matan su 106 gami da namiji guda cikin murna da annashuwa.
A halin da ake ciki dai daliba guda ce mai suna Leah Sharibu, wacce Kirista ce 'yan Boko Haram din basu sako ba.
A ranar 19 ga watan Fabarairu da ya gabata ne mayakan na Boko Haram suka sace 'yan matan su 111, kafin daga bisani su sako su a ranar Laraba data gabata, amma an ce biyar daga cikin sun mutu a cikin wani yanayi da ake zaton na matsatsi ne.
Daga nan ne kuma aka garzaya da 'yan matan a fadar gwamnati dake Abuja, babban Birnin Najeriyar inda har suka gana da shugaba Muhammadu Buhari.