Gwamnatin Mali Ta Jaddada Aniyarta Ta Yaki Da Ayyukan Ta'addanci A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29428-gwamnatin_mali_ta_jaddada_aniyarta_ta_yaki_da_ayyukan_ta'addanci_a_kasar
Fira ministan Mali ya bukaci hadin kan kasa a Mali tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:37+00:00 )
Mar 28, 2018 08:03 UTC
  • Gwamnatin Mali Ta Jaddada Aniyarta Ta Yaki Da Ayyukan Ta'addanci A Kasar

Fira ministan Mali ya bukaci hadin kan kasa a Mali tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.

Fira ministan Mali Soumeylou Boubeye Maiga a ziyarar aikin da ya kai zuwa yankin arewacin kasar ya bayyana cewa: Rundunar sojin kasar da hadin gwiwar sojojin kasar Faransa suna ci gaba da gudanar da sintiri a yankunan arewacin kasar da nufin murkushe duk wata barazanar ta'addanci.

Har ila yau fira ministan kasar ta Mali ya bukaci hadin kan al'ummar Mali wajen taimaka wa jami'an tsaron kasar a yankin da suke yi da gungun 'yan ta'adda musamman a yankunan garuruwan Gao da Mabako.