Nijar : An Kori Wasu Kansilolin Zinder
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29516-nijar_an_kori_wasu_kansilolin_zinder
Gwamnatin Nijar ta sanar da kokar wasu shugabannin kananan hukumomi uku da suka hada da na Guidimuni da Mirriah da kuma Dantchiao, duka a jihar Zinder saboda tafka manyan kura kurai.
(last modified 2018-08-22T11:31:38+00:00 )
Mar 31, 2018 10:38 UTC
  • Nijar : An Kori Wasu Kansilolin Zinder

Gwamnatin Nijar ta sanar da kokar wasu shugabannin kananan hukumomi uku da suka hada da na Guidimuni da Mirriah da kuma Dantchiao, duka a jihar Zinder saboda tafka manyan kura kurai.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne a yayin taron majalisar ministocinta na jiya Juma'a 30 ga watan Maris 2018, karkashin jagorancin shugaban kasar Alhaji Isufu Mahamadu.

Saidai ba'a yi karin haske ba kan laifukan da ake tuhumar kansilolin da aikatawa ba.

Sanarwa da gwamnatin ta fitar ta kuma sanar da kafa tawaga ta musamman da ta za ta tafiyar da  kananan hukumomin Tesker a jihar ta Zinder, da kuma a Dakoro dake jihar Maradi.