An Bukaci Ficewar Sojojin Sudan Daga Kawancen Saudiya A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29558-an_bukaci_ficewar_sojojin_sudan_daga_kawancen_saudiya_a_yemen
'Dan majalisar dokokin kasar Sudan ya bukaci kasarsa ta janye sojojinta daga cikin jerin kawancen kasashen larabawa bisa jagorancin kasar Saudiya a Yemen.
(last modified 2018-08-22T07:01:38+00:00 )
Apr 02, 2018 01:56 UTC
  • An Bukaci Ficewar Sojojin Sudan Daga Kawancen Saudiya A Yemen

'Dan majalisar dokokin kasar Sudan ya bukaci kasarsa ta janye sojojinta daga cikin jerin kawancen kasashen larabawa bisa jagorancin kasar Saudiya a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalto Abdul Rahman al-Fudail dan majalisar dokokin kasar Sudan daga bangaren jam'iyar Al-Islah Al-An a jiya lahadi na cewa, a halin da ake cikin kasar Sudan ta shiga cikin wani yanayi amma babu wata kasa daga cikin wannan kawance da ya taimakawa kasar,kuma ko a gaba ba za su taimaka mata ba, saboda wannan dalili ya zama wajibi kasar ta janye sojojinta daga cikin jerin kawancen kasashen larabawa karkashin jagorancin saudiya dake yakar al'ummar kasar ta Yemen.

A watanin baya-bayan nan, gwamnatin kasar Sudan na ci gaba da fuskanta suka,kan aikewa da sojojin kasar zuwa kasar Yemen.

Daga watan Maris shekarar 2015, kimanin sojoji dubu hudu ne kasar Sudan ta aike zuwa kasar Yemen, cikin jerin kawancen kasashen larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiya da suke kai hare-haren wuce gona da irin kan al'ummar kasar, kuma ya zuwa yanzu an hallaka sojojin sudan 412 yayin da aka jikkata wasu dariruwa na daban.