Kamaru : An Ceto 'Yan Kasashen Waje 12 Da Ake Garkuwa Da Su
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29618-kamaru_an_ceto_'yan_kasashen_waje_12_da_ake_garkuwa_da_su
Hukumomin Kamaru sun ce sojojin kasar sunyi nasara ceto wasu 'yan kasashen waje 12 da akayi garkuwa dasu a yankin masu magana da turancin Ingilishi.
(last modified 2018-08-22T07:01:39+00:00 )
Apr 04, 2018 06:49 UTC
  • Kamaru : An Ceto 'Yan Kasashen Waje 12 Da Ake Garkuwa Da Su

Hukumomin Kamaru sun ce sojojin kasar sunyi nasara ceto wasu 'yan kasashen waje 12 da akayi garkuwa dasu a yankin masu magana da turancin Ingilishi.

Mutanen da aka ceton wadanda galibi 'yan yawan bude ido ne sun hada da 'yan asalin kasashen Italiya da kuma na Swiss a cewar wata sanarwar gwamnatin kasar.

An dai ceto mutanen ne a ranar Litini, saidai babu karin haske akan lokacin da akayi garkuwa dasu, saidai sanarwar ta ce wani gungun 'yan ta'adda ne sukayi garkuwa da mutanen a yankin Mungo-Ndor.

Ko baya ga hakan sanarwar ta ce an kuma kubutar da wasu kansilolin kasar ta Kamaru su guda shida a wani samamen soji a yankin arewa maso yammacin kasar.