Chadi Za Ta Gina Wajen Adana Man Fetur Na Farko
Shugaban kasar Chadi Idris Debey ne ya sanar da shirin gina wurin ajiye man fetur din domin magance matsalar da ka ita kunno kai ta karancin mai
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto shugaban kasar ta Chadi yana ci gaba da cewa; Za a gina wurin ajiyar man ne a kusa da matatar Jarmaya da mai nisan kilo mita 35 daga babban birnin kasar Njamina.
Shugaban na Chadi ya ci gaba da cewa; Idan an kammala ginin rumbun adana man, za a rika ajiye man da ake bukatuwa da shi a kasar na tsawon shekaru biyu, saboda idan matatar mai ta sami matsala, ba za a sami tsaiko ba wajen wadata kasa da makamashi.
An gano man fetur ne a kasar Chadi a 1999, sannan kuma aka fara hako shi a 2003. A kowace rana ta Allah Chadin na fitar da ganga dubu dari da saba'in.