An Hana 'Yan Wasan Isra'ila Shiga Kasar Tunusiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29664-an_hana_'yan_wasan_isra'ila_shiga_kasar_tunusiya
Wata Kotu a Tunusiya ta haramtawa 'yan wasan Haramtacciyar kasar Isra'ila shiga kasar don halartar wasan Taekwondo.
(last modified 2018-08-22T11:31:39+00:00 )
Apr 06, 2018 06:28 UTC
  • An Hana 'Yan Wasan Isra'ila Shiga Kasar Tunusiya

Wata Kotu a Tunusiya ta haramtawa 'yan wasan Haramtacciyar kasar Isra'ila shiga kasar don halartar wasan Taekwondo.

A jiya alhamis ne kotun ta yanke wannan hukunci, bayan da tawagar kasar mai yaki da dawo da alaka tsakanin kasar da HKI ta shigar da karar kungiyar wasan kwallon Taekwondo ta kasar, inda ta bukaci kotun ta hana kungiyar kirar 'yan wasan HK Isra'ila da kuma haramta musu shiga cikin kasar.

A wannan juma'a ce za a fara gasar kasa da kasa na wasan Taekwondo a kasar ta Tununsiya kuma za a kamala a ranar 13 ga wannan wata na Avrilu da muke ciki.

Kafin hakan dai, kungiyar wasan Taekwondo na Duniya ta fitar da sunayen 'yan wasan da suka halarci wannan gasa ciki, kuwa har da 'yan wasan Isra'ila guda 4, lamarin da ya yi sanadiyar fuskantar martani mai tsanani daga al'ummar kasar ta Tunusiya.