Afrika Ta Kudu : An Dage Zaman Shari'ar Jacob Zuma
Kotun birnin Durban, a Afrika Ta Kudu, ta dage zaman shari'ar da ake wa tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma, har zuwa ranar 8 ga watan Yuli mai zuwa.
Yau Juma'a ne dai Mista Zuma, ya gurfana gaban babbar kotun Durban, bisa zargin cin hanci da rashawa kan wani cinikin makamai a shekarar 1990.
Lauyoyin gwamnati ne da na tsohon shugaban kasar ne suka bukaci dage zaman shari'ar, mintina kadan bayan da Mista Zuma din ya bayyana gaban kotun.
Mista Zuma yana fuskantar tuhuma 16 da suka hada da rashawa da zamba da almundahana da hallata kudaden haram, saidai yana mai musunta duk wadannan zarge zargen.
Bayan fitowarsa, Zuma ya bayyana wa magoya bayansa da sukayi cincirindo gaban kotun cewa, babu wata hujja da ake da ita game da tuhumar da ake masa.