Shugaban Kasar Tunusiya Ya Ce: Tunusiya Tana da Cikakken Yancin Kai
Shugaban kasar Tunusiya ya bayyana cewa: Duk da matsalolin da Tunusiya take fuskanta gami da matsin lamba a wasu bangarori amma kasar tana da cikakken yancin kai.
A jawabinsa a taron tunawa da cikan shekaru goma sha takwas da mutuwar tsohon shugaban kasar Habib Bourguiba da ya jagoranci samun 'yancin kasar daga turawan mulkin mallaka a jiya Juma'a: Shugaban Tunusiya Beji Sayyid Essebsi ya bayyana cewa: Kasar tunusiya tana alfahari da irin gagarumin ci gaba da ta samu a bangarori da dama a tsawon tarihinta duk kuwa da wasu 'yan matsaloli da matsin lamba da take fuskanta nan da can.
Beji Sayyid Essebsi ya kara da cewa: Tun daga gwagwarmayar neman yancin kai har zuwa zamar kasar mai cikakken yancin kai an samu ci gaba a bangarori da dama, duk kuwa da cewa: Wasu jama'a da kungiyoyi a cikin kasar basu ganin haka.
A jiya Juma'a ce gwamnatin Tunusiya da al'ummar kasar suka gudanar da bikin tunawa da marigayi Habib Bourguiba da ya jagoranci fafatukar neman 'yancin kan kasar ta Tunusiya, kuma ya shugabancin kasar tun daga shekara ta 1957 zuwa 1987 sannan ya mutu a ranar 6 ga watan Aprilun shekara ta 2000.