An Bukaci Uganda Da Ta Ba Da Kariya Ga 'Yan Gudun Hijira
Majalisar Dinkin Duniya ce ta yi kiran ga gwamnatin kasar Uganda da ta kare 'yan gudun hijirar bayan kisan da aka yi wa wani karamin yaro dan kasar Sudan ta kudu
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Uganda na jaddada wajabcin ba da kariya ga 'yan gudun hijirar.
A ranar 29 ga watan Maris ne aka tsinci gawar karamin yaron dan shekaru biyu a yankin Lamwo da ke arewacin kasar ta Uganda. Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan hakikanin abin da ya faru da karamin yaron dan gudun hijira da ya fito daga kasar Sudan ta kudu.
Majiyar Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce; Kaso uku cikin hudu na 'yan guudn gudun hijirar kasar Demokradiyyar Congo da suke a cikin kasar Uganda, knanan yara ne.