An Hallaka 'Yan Ta'adda Biyar A Mali
(last modified Sun, 08 Apr 2018 19:02:31 GMT )
Apr 08, 2018 19:02 UTC
  • An Hallaka 'Yan Ta'adda Biyar A Mali

Dakarun hadaka dake kasar Mali sun sanar da hallaka 'yan ta'adda biyar a wani sumeme da suka kai sansaninsu a kusa da garin Tombouctou na arewacin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Kanal Patrik Steiger kakakin rundunar sojin Faransa dake kasar Mali na cewa dakarun kasar Faransa dake yankin Sahel wata Bakhan sun kai sumamen ba zata kan sansanin 'yan ta'adda dake da nisan kilomita 120 daga garin Tombouctou a arewacin kasar tare da hallaka biyar daga cikinsu.

A ranar 1 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki, Dakarun kasar Faransa tare da hadin gwiwar na kasar ta Mali sun hallaka kimanin 'yan ta'adda 30 a kusa da kan iyakar kasar da jamhoriyar Nijer.

Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro tun a 2012 bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, da kuma kutsen masu tsaurin ra'ayi a arewacin kasar.

A shekarar 2013 kuma, masu tsattsauran ra'ayin sun watsu cikin sassann arewacin kasar bayan shigar sojojin Faransa da MDD.