An Zarkin Wasu Kasashen Afirka Da Taimakawa 'Yan Tawayen Mali
(last modified Sun, 08 Apr 2018 19:06:37 GMT )
Apr 08, 2018 19:06 UTC
  • An Zarkin Wasu Kasashen Afirka Da Taimakawa 'Yan Tawayen Mali

Wata majiya a kasar Mali, ta bayyana cewa wasu kasashen yankin ne ke bayar da horo da kuma bayar da makamai ga masu kai hari a kasar

Gidan radion kasa da kasa na Faransa ya nakalto  Claudio Gramizzi mai kula da bangaren yammacin Afirka a cibiyar bincike kan rikici da makamai ya ishara kan yadda wasu kasashen yankin ke taimakawa kungiyoyi masu dauke da makamai a bayan fage, inda ya tabbatar da cewa, tabas akwai wasu kasashe a yankin dake bayar da horo da kuma makamai ga masu tayar da kayar baya a kasar ta Mali.

 Gramizzi ya ce wadannan mutane dake bayar da horo ga masu tayar kayar bayan cikin sauki suke shiga kasar ta Mali suna aikata wannan aika-aika kuma hakan babbar  barazana ga harakokin tsaron kasar ta Mali.

Har ila yau Mista  Claudio Gramizzi ya tabbatar da cewa mafi yawan makaman da masu tayar da kayar bayan ke kai hari da su , su fito ne daga runbun tsimin makamai na jami'an tsaron yankin.

To saidai jami'in bai bayyana kasar da wannan makamai ke fitowa ba.