Mali: An Kashe 'Yan Takfiriyyah Biyar A Kusa Da Tambutu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29756-mali_an_kashe_'yan_takfiriyyah_biyar_a_kusa_da_tambutu
Kakakin Sojan Faransa a kasar Mali Patrik Steiger ne ya sanar da haka, ba tare da yin cikakken karin bayani akan yadda lamarin ya afku ba
(last modified 2018-08-22T07:01:40+00:00 )
Apr 09, 2018 04:47 UTC
  • Mali: An Kashe 'Yan Takfiriyyah Biyar A Kusa Da Tambutu

Kakakin Sojan Faransa a kasar Mali Patrik Steiger ne ya sanar da haka, ba tare da yin cikakken karin bayani akan yadda lamarin ya afku ba

A ranar 30 ga watan Aprilu ma, sojojin Faransa da suke a kasar Mali sun kashe masu akidar kafirta musulmi 30 a yankin Akabar da ke kusa da iyakar jamhuriyar Nijar.

Jami'an tsaron kasar Mali sun yi nasarar tarwatsa kungiyar masu kafirta musulmi tun a 2013, tare da kwace ikon da suke da shi a cikin wasu yankunan arewacin kasar.Sai dai har yanzu da akwai wasu yankuna wadanda'yan ta'addar suke da karfi.

Da akwai sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da kuma na Faransa a cikin sassan kasar ta Mali.