Kakakin Majalisar Dokokin Somaliya Yayi Murabus Kafin Kada Kuri'ar Korarsa
(last modified Mon, 09 Apr 2018 11:05:19 GMT )
Apr 09, 2018 11:05 UTC
  • Kakakin Majalisar Dokokin Somaliya Yayi Murabus Kafin Kada Kuri'ar Korarsa

Kakakin majalisar dokokin kasar Somaliya, Mohamed Sheikh Osman Jawari, yayi murabus daga mukaminsa jim kadan kafin 'yan majalisar su kada kuri'ar rashin amincewa da shi, lamarin da ya kawo karshen rikicin na siyasa da ake fama da shi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo daya daga cikin 'yan majalisar, Dahir Amin Jesow, yana fadin cewa 'yan majalisar suna zaune suna shirin fara kada kuri'ar rashin amincewa da kakakin majalisar kenan sai, mataimakin kakakin ya karanto takardar yin murabus din kakakin. Dan majalisar ya ce majalisar ta cika da murna bayan karanta takardar murabus din kakakin, lamarin da ya kawo karshen rikicin makonni da kasar ta shiga.

Rikici dai ya kunno kai tsakanin suran 'yan majalsar da shugaban majalisar wanda yake rike da wannan mukamin tun a shekara ta 2013 ne bayan da kakakin ya janye daftarin da aka gabatar na tsige tsohon shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud a 2015, lamarin da ya sanya kasar cikin rikici na siyasa.

Tun a shekarun 1990 ne dai kasar Somaliyan ta shiga cikin mawuyacin hali na rashin tsaro da rashin tabbas na siyasa.