Amurka Ta Cire Chadi Daga Cikin Kasashen Da Ta Hanawa Yin Hijira
Apr 11, 2018 07:52 UTC
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato majiyar gwamnatin Amurkan tana sanar da cire 'yan kasar Chadi daga cikin jerin kasashen da ta hanawa yin hijira zuwa Amurka.
Daukar matakin na cire Chadi,ya biyo bayan rahoton da ake fitarwa a kasar ta Amurka ne duk bayan watanni shida da ma'aikatar harkokin waje take yi.
Shugaban kasar Amurka Dodanld Trump ne ya shelanta sunaye wasu kasashe da mafi yawancinsu na musulmi ne a matsayin wadanda ya haramtawa shiga cikin Amurka.
Baya ga kasar Chadi, sauran kasashen da Amurka ta dauki tsauraran matakai ga 'yan kasar idan za su yi hijira zuwa cikinta, su ne Iran, Libya, Syria, Venezuela, Korewa ta Arewa, Somaliya da kuma kasar Yemen.
Tags