Kimanin Mutane 257 Suka Rasu Sanadiyar Hadarin Jirgin Soja A Aljeriya
Apr 11, 2018 11:16 UTC
Hukumomin Aljeriya sun sanar da mutuwar mutane 257 sanadiyar hadarin jirgin soja a kasar
Cikin wata sanarwarwa da suka fitar a wannan laraba, hukumomin birnin Alge na kasar Algeriya sun bayyana cewa kimanin mutane 257 suka rasa rayukansu sanadiyar hadarin jirgin soja a kusa da filin sauka da tashi na Boufarik dake arewacin kasar, kuma yawa daga cikin wadanda hadarin ya ritsa da su, jami'an tsaro ne.
Wata majiyar tsaron kasar ta Aljeriya ta tabbatar da mutuwar dukkanin wadanda ke cikin jirgin, kuma ya zuwa yanzu ba dalilin faduwar jirgin.
Jirgin dake dauke da jami'an tsaro kimanin dari biyu, ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga filin jirkin Boufarik dake kudancin kasar.
Tags