UNICEF:'Yan Boko Haram Sun Sace Yara Sama Da 1000 A Najeriya
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce daga shekarar 2013 zuwa yanzu mayakan boko haram sun sace yara sama da dubu daya a arewa maso gabashin Najeriya.
A wani rahoto da UNICEF ta fitar,yayin tunawa da shekara hudu da sace 'yan matan Sakandaren Chibok sama da 200 a jihar Borno, asusun ya ce an ci gaba da kai hare-hare kan yara da sace su.
Shugaban hukumar ta UNICEF a Nijeriya, Mohamed Malick Fall ne ya sanar da hakan inda yace kananan yara a yankunan arewa maso gabashin Nijeriyan suna ci gaba da fuskantar barazana daga wajen 'yan kungiyar, inda yace hukumar tasa ta sami tabbaci cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun sace samar da yara 1000 wanda akwai yiyuwar adadin ya dara haka sosai ma.