An Cika Shekaru Hudu Da Sake 'Yan Matan Chibok
(last modified Sat, 14 Apr 2018 06:25:32 GMT )
Apr 14, 2018 06:25 UTC
  • An Cika Shekaru Hudu Da Sake 'Yan Matan Chibok

Yau 14 ga watan Afrilu, aka cika shekaru hudu cif da sake 'yan matan makarantar sakandare na garin Chibok a arewa maso gabashin Najeriya.

a irin wannan ranar ce a shekarar 2014 mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan sakandaren Chibok sama da 200 a garin na Chibok.

Sama da 100 daga cikin 'yan makarantar suka tsere daga hannun 'yan Boko Haram ko wadanda dakarun kasar suka kubutar ta hanyar tattaunawar gwamnati da masu shiga tsakani.

Batun sace 'yan matan na Chibok dai a lokacin tsohuwar gwamnatin Goodluk Jonatan ya tayar da zazzafar muhawara a cikin da wajen kasar ta Najeriya.