Gambiya : Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi
(last modified Sat, 14 Apr 2018 06:28:07 GMT )
Apr 14, 2018 06:28 UTC
  • Gambiya : Jam'iyya Mai Mulki Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi

Jam'iyya mai mulki a kasar Gambiya ta lashe da gagarimin rinjaye zaben wakilan kananan hukumomi da aka gudanar.

Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna cewa, jam'iyyar UDP mai mulki ta shugaba Adama barrow ta lashe zaben da gagarimin rinjaye, inda ta samu kananan hukumomi 62.

Sai Jam'iyyar GDC ce ta jagoran 'yan adawa ce ke biya mata da kananan hukumomi 23, a cewar sakamakon da shugaban hukumar zaben kasar, Alieu Momar Njie ya sanar a jiya Juma'a.

Zabubukan wadanda su ne na farko tun bayan mulkin tsohon shugaba Yahyah Jammet na da manufar sabunta wakilai a kananan hukumomi 120 na kasar.