Najeriya: Shekara hudu da sace 'yan matan Chibok
(last modified Sat, 14 Apr 2018 12:36:03 GMT )
Apr 14, 2018 12:36 UTC
  • Najeriya: Shekara hudu da sace 'yan matan Chibok

Yau 14 ga watan Afrilu, aka cika shekaru hudu cif da sake 'yan matan makarantar sakandare na garin Chibok a arewa maso gabashin Najeriya.

A irin wannan ranar ce a shekarar 2014 mayakan Boko Haram suka sace 'yan matan  sakandaren Chibok sama da 200 a garin na Chibok.

daga cikin su sama da 100 daga cikinsu  suka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram din  ta hanyar gudu ko kuma  wadanda dakarun kasar suka kubutar ta hanyar tattaunawar gwamnati da masu shiga tsakani.

To amma an dauki lokaci har bayan shudewar gwamnatin Jonathan din babu wata ko daya daga cikin 'yan matan da aka kubutar.

Batun sace 'yan matan na Chibok dai a lokacin tsohuwar gwamnatin Goodluk Jonatan ya tayar da zazzafar muhawara a cikin da wajen kasar ta Najeriya.