Aljeriya: An Fake Da Karya Wajen Kai Wa Syria Hari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29924-aljeriya_an_fake_da_karya_wajen_kai_wa_syria_hari
Wani Masanin harkokin tsaro na kasar Aljeriya ya bayyana cewa; An Kirkiri babbar karya ne ta makamai masu guba domin kai wa Syria hari
(last modified 2018-08-22T07:01:42+00:00 )
Apr 15, 2018 06:36 UTC
  • Aljeriya: An Fake Da Karya Wajen Kai Wa Syria Hari

Wani Masanin harkokin tsaro na kasar Aljeriya ya bayyana cewa; An Kirkiri babbar karya ne ta makamai masu guba domin kai wa Syria hari

Bin Umar Bin Janah ya ci gaba da babu yadda za a iya kare harin da kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa su ka kai wa Syria, domin batun amfani da makami mai guba karya ce da aka kirkira.

Bin Janah ya kara da cewa; Harin ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma babu abin da zai haifar sai kara hargitsa yanayin gabas ta tsakiya.

Kafafen watsa labarun yammacin turai sun rika riya cewa Syria ta yi amfani da makamai masu guba a yankin Doma, abin da ta kasashen Faransa da Birtaniya da Amurka su ka kai mata hari.

Tuni dai gwamnatin kasar ta Syria ta karyata zargin da aka yi mata na cewa ta yi amfnai da makamai masu guba.