An Sake Cafke Masu Zanga zanga A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30002-an_sake_cafke_masu_zanga_zanga_a_nijar
Rahotanni daga jamhuriya Nijar na cewa an cafke mutane da dama ciki har da wasu mambobin kungiyoyin fara hula biyu, biyo bayan haramtacciyar zanga zangar da aka gudanar a Yamai babban birnin kasar a jiya Lahadi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 16, 2018 01:52 UTC
  • An Sake Cafke Masu Zanga zanga A Nijar

Rahotanni daga jamhuriya Nijar na cewa an cafke mutane da dama ciki har da wasu mambobin kungiyoyin fara hula biyu, biyo bayan haramtacciyar zanga zangar da aka gudanar a Yamai babban birnin kasar a jiya Lahadi.

'Yan kungiyoyin sun hada da Diori Ibrahim mamba a kungiyar (AEC) da kuma Maikul Zodi na wata kungiyar fara hula, sai kuma wata 'yar jarida mai suna Samira Sadu.

Kungiyoyin fara hula hular dai sun kira a fito zanga zangar da kuma zaman dirshin da mahukuntan birnin suka haramta.

An dai shafe makwanni da dama kungiyoyin na jerin zanga zanga da zaman dirshin kan yin tir da sabuwar dokar haraji dake kunshe a kasafin kudin kasar na 2018, saidai a baya bayan nan hukumomin birnin sun haramta duk wata zanga zanga makamancin hakan saboda a cewarsu dalilai na tsaro da barazanar ta'addanci.

Dama kafin hakan akwai jagororin kungiyoyin fara hula da dama da ake tsare a gidan kaso bisa saba wa dokar haramta zanga zanga.