Jakadan Cote De Voire A Majalisar Dinkin Duniya Ya Rasu
(last modified Thu, 19 Apr 2018 12:26:55 GMT )
Apr 19, 2018 12:26 UTC
  • Jakadan Cote De Voire A Majalisar Dinkin Duniya Ya Rasu

kamfanin dillancin labarun faransa ya ambato majiyar diplomasiyya na cewa; Jadakan kasar Cote De Voire a Majalisar Dinkin Duniya Bernard Tanoh Boutchoue ya rasu a asibitin birnin New york.

Bernard Tanoh-Boutchoue ya kama aiki ne a Majalisar Dinkin Duniya a cikin watan Disamba bayan da ya baro kasar Rasha da ya yi aikin diplomasiyya.

Makwanni biyu da su ka shude, Bernard Tanoh-Boutchoue ya ki kada kuri'ar goyon bayan ina da yakin kasashen turai da Amurka akan kasar Syria.

Gabanin rasuwarsa Bernard Tanoh-Boutchoue yana daga cikin fitattun jami'an diplomasiyyar kasarsa, inda ya yi aiki a kasashen Armenia, Khazakhistan, Kyrkizstan da Tajikistan.