Shugaba Sudan Al-Bashir Ya Kori Ministan Harkokin Wajen Kasar
(last modified Sat, 21 Apr 2018 05:44:33 GMT )
Apr 21, 2018 05:44 UTC
  • Shugaba Sudan Al-Bashir Ya Kori Ministan Harkokin Wajen Kasar

Shugaban kasar Sudan Omar Hasan al-Bashir ya kori ministan harkokin wajen kasar Ibrahim Ghandour, a wani abin da ake gani ya samo asali ne saboda korafin da yayi kan rashin biyan jami'an diplomasiyyar kasar da suke waje albashi na watanni.

Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan din SUNA ya bayyana cewar ya kori Farfesa Ibrahim Ghandour daga mukamin ministan harkokin wajen kasar, duk kuwa da cewa kafar watsa labaran ba ta fadi dalilin da ya sanya shugaba Al-Bashir din daukan wannan matsaya ba.

A wani jawabi da yayi ranar Larabar da ta gabata, tsohon minista Ghandour ya ce ma'aikatar ta sa ta gaza wajen biyan bukatu da kuma albashin ma'aikatan diplomasiyyar da suke kasashen waje sakamakon siyasar tsuke bakin aljihu da gwamnatin ta shigo da shi, lamarin da ake ganin ya fusata shugaba Al-Bashir din da ya sanya ya kore shi daga aiki.

Kasar Sudan din dai tana fuskantar matsalar tattalin arziki bugu da kari kan karancin kudaden kasashen waje musamman dalar Amurka lamarin da ya sanya rayuwa ta ke ci gaba da wahala ga al'ummar kasar.