An Kashe Yan Ta'adda 15 A Tsakiyar Kasar Mali
(last modified Sat, 21 Apr 2018 19:05:41 GMT )
Apr 21, 2018 19:05 UTC
  • An Kashe Yan Ta'adda 15 A Tsakiyar Kasar Mali

Majiyar sojojin kasar Mali ta bada sanarwan cewa sojojin kasar sun sami nasarar hallaka yan ta'adda 15 a wani sumamen da suka kai masu a garin Mupik a tsakiyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar sojojin kasar ta Mali tana fadar haka a yau Asabar. Ta kuma kara da cewa sojojin sun kai wannan sumamen ne a ranar Jumma'a a garin na Mupik inda suka yiwa yan ta'adda ba zata, suka kashe mutum 15 daga cikinsu sannan wasu biyu suka ji rauni. Majilar ta kara da cewa sojojin sun gano makamai masu yawa a mamuyan yan ta'adda a garin 

a cikin yan makonnin da suka gabata an sha samun tashe-tashen hankula a tsakiyar kasar ta Mali inda mutane da dama suka rasa rayukansu. Tun shekara ta 20154 ne dai mayakan kungiyoyin yan ta'adda daban daban suka fara kai hare-hare a yankunan tsakiyar kasar ta Mali duk da cewa wasu daga cikin kungiyoyin yan tawayen kasar sun cimma sulhu tare da gwamnatin kasar a shekara ta 2015 din.