Aljeriya : FLN, Ta Bukaci Bouteflika, Ya Nemi Wa'adi Na 5
Apr 22, 2018 11:15 UTC
Jam'iyyar FLN mai mulki a Aljeriya, ta bukaci shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika, da ya yi tazarce ta hanyar neman wani wa'adin mulki karo na biyar, duk da rashin lafiyar da yake fama da shi.
Kiran da sakataren jam'iyyar ta FLN, Djamel Ould Abbes, ya yi nada manufar ci gaba da samar da tsaro da samar da makoma mai kyau ga matasan kasar.
Duk da a cewarsa maganar karshe na ga shugaban kasar mai shekaru 81.
Tun a shekara 1999 ne shugaba Bouteflika ya ke rike da madafun ikon kasar ta Aljeriya, saidai kawo yanzu shugaban ya fara nuna alamun gajiya saboda rashin lafiyar kwakwaluwa da ya fuskanta, wanda ya sa ba'a cika ganinsa ba bainar jama'a.
Tags